IQNA

An Saka Bakar Tuta A Haramin Imam Ridha Don Makokin Kisan Kiyashi a  Asibitin Gaza

Tehran (IQNA) – Sakamakon ci gaba da laifuffukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan al’ummar Gaza, musamman harin da ta kai a wani asibiti da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 500, a yau ranar 18 ga watan Oktoban an saka bakaken tutoci a Haramin Imam Ridha a Mashhad domin makoki.